Furodusa Abdul Amart ya saya wa dattawan jarumai 50 fom don sabunta rajistar su a Kannywood

hhh
0
 BABBAN furodusa a Kannywood kuma shugaban kamfanin shirya finafinai na Abnur Entertainment, Alhaji Abdul Amart Mohammed, ya É—auki nauyin saya wa wasu jarumai dattijai kimanin hamsin fom na sabunta rajistar su a masana’antar.

 Tun a shekarar da ta gabata aka fara sayar da fom É—in don sabunta rajistar ‘ya’yan masana’antar, wanda daga baya aka dakatar. A cikin wata sanarwa da mujallar Fim ta samu É—auke da sa-hannun darakta Isma’il Khalil Ja’en, an bayyana sunayen jaruman da Amart ya saya wa fom É—in.

 Sun haÉ—a da Hussaini Sule ƘoÆ™i, Malam Inuwa Iliyasu, ÆŠan Azimi Baba, Hamisu Sogiji, Malam Labaran, Auwalu Marshall, Umar B. Hankaka, Bashir Bala Ciroki, Bashir Nayaya, Malam Haruna Aliyu, Hajiya Tambaya, Mama Duduwa, Hajiya Zulai Bebeji, Hafsat Iliyasu, Ladidi Fagge, Hajara Usman, da Lubabatu Madaki. Akwai kuma Muntari Bandaru, Jibrin Laku-Laku, Safiya Kishiya, Maryam CTV, Habibu Yaro, Idris Didi, Bilkisu Maigado, Malam Auwalu Dare, Tela na cikin shirin ‘Hankaka’, Hajara Abubakar (DumÉ“aru), Hajiya Sadiya Gaida, Amina M. Idris, A’isha Abubakar, Bilkisu Musa, Sani Abubakar, Hauwa Muhammad, Hajiya Rahama Gaida, Adamu Yusuf Balantiya, Auwalu B. Hotoro, Auwalu Zo-Mu- LeÆ™a, Hajiya Aisha Muhammad, Suwaiba Abubakar Makauniya, Baba Hasin da Bilkin RK.


 Sanarwar ta ce akwai sauran jarumai 10 da ba a kammala tantancewa ba, da zarar an kammala za a saki sunayen su da yardar Allah. Sanarwar ta buÆ™aci duk wanda ya ga sunan sa a cikin jerin sunayen da ya hanzarta zuwa ofishin MOPPAN domin karÉ“ar nasa fom É—in. Ana ci gaba da sayar da fom na kowane rukunin Æ™ungiyoyin fim na Kano, kama daga Æ™ungiyar daraktoci, furodusoshi, ‘yan wasa, masu kyamara, mawaÆ™a da sauran su. Ana samun fom É—in ne a ofishin MOPPAN da ke Titin Sabuwar Jami’ar Bayero, Ƙofar Famfo, kusa da ofishin Isma’il Khalil Ja’en. 

A ɓangaren jarumai, an bayyana cewa za su samu nasu a wurin shugabannin su ko su tuntuɓi Alhassan Kwalle kai-tsaye. Sanarwar ta ce za a rufe sayar da fom ɗin ranar Talata mai zuwa, 20 ga Fabrairu, 2024.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)