Ibrahim Mandawari na so duk ‘yan Kannywood su ba Ali Nuhu cikakken goyon baya

0
DATTIJO a Kannywood kuma Mai’unguwar Mandawari, Alhaji Ibrahim Mandawari, ya tofa albarkacin bakin sa game da taron taya Ali Nuhu samun muƙami da aka yi. Shahararren jarumin ya jinjina wa waɗanda su ka yi ruwa da tsaki wurin ganin an tsara taron yadda ya kamata.

 Haka kuma ya ja hankalin abokan sana’ar baki ɗaya da su ba Ali Nuhu goyon baya ɗari bisa ɗari. Dattijon ya yi waɗannan bayanan ne a wani faifan murya da ya tura a cikin guruf ɗin da aka buɗe na musamman don shirya taron taya murnar, wanda kusan duk ‘yan fim na ciki na da da na yanzu, mai suna Sarki Ali Nuhu Congratulatory Dinner.

 Mandawari ya fara da cewa: “A’uzu billahi minash shaiɗanir rajim. Bismillahir rahamanir rahim. Wasallahu ala nabiyul karim. ‘Yan’uwa abokan sana’a salamu alaikum. Suna Ibrahim Muhammad Mandawari, ɗaya daga cikin ku, kuma Mai’unguwar Mandawari. 

“Babu shakka taron nan, babu abin da ɗan masana’antar nan zai ce, illa ya ce alhamdu lillahi, ya gode wa Allah, saboda taron ya haifar da abubuwa da yawa, kuma muhimmin magana na shi ne cewa an yi zumunci, an taru an ga juna, wani ka shekara biyar, wani goma ba ka gan shi ba, kuma an girmama juna. “Allah ya gani, ni da na zauna da farko a teburin elders, daga baya aka mai da ni sama, kusa wato da na rinƙa gaisawa, waɗanda su ka rinƙa zuwa su na gaishe ni, abin ya ba ni sha’awa, ya ba ni mamaki, kuma na ji daɗi ƙwarai-ƙwarai da gaske.

 “Wannan ne ya sa kullum na ke yaƙi da duk mutumin da zai ce masana’antar ba a da mutunci ko ba a da tarbiyya ko ba a da kaza. Ni ban yarda ba. Kuma ban yarda da a rinƙa cin mutuncin mata ko mata zalla ba. Ba a yi masu adalci, duk da cewa akwai abubuwan da ya kamata su ma su gyara. To wannan kenan.” Ya ci gaba da cewa, “Ina roƙon organisers na wannan, daga kan ita Hajiya Hindatu Bashir da sauran abokan aikin, su Muddassir Ƙassim, su Ghali DZ, su Lilo da ire-iren su, yadda su ka shirya wannan abin alkhairi, to a yi ƙoƙari a ga cewa an yi maintaining . 

Bayan wannan gaishe-gaishe da ake yi a platform ɗin nan, a yi ƙoƙari iyakacin iyawa a ga cewa an samar da wasu abubuwa da zumuncin nan zai ɗore, kuma ya zama sila na haɓakar wannan masana’anta. Na biyu kenan.” “Na uku kuma na ƙarshe shi ne, kada mu yi murnar karen ɓuki, mu taya ɗan mu murna Allah ya ba shi matsayi, to wajibi mu ba shi haɗin kai in ya zo da wasu policies da tsare-tsare, to ya kamata don Allah kowane memba ya nuna shi ɗa ne, a ba shi haɗin kai. “Shi ma kan sa na nan Kano, Abba El-Mustapha, da ya rabauta da wancan matsayi, shi ma a ba shi haɗin kai. 

Idan rajista ce, a daure a yi, in wani abu ne, wata doka, a daure a bi. Wannan ne zai daɗa tabbatar da mutuncin mu. “Kuma na tabbatar da Ali ba baƙon mutanen kudancin ƙasar nan ba ne, ya daɗe ya na hulɗa da su. Ni kai na mun je Legas da shi mun yi aktin kusan shekaru ashirin da su ka wuce, ina tsammani lokacin bai ma yi auren fari ba. Kenan ya saba da su, ya san yadda zai yi hulɗa da su. “Za su sa masa pressure , su ce kada ya nuna son kai, su ‘yan Kudu ne, shi daga Arewa, amma na tabbatar duk dabarun da zai yi ya taimaka wa Kannywood zai. 

To a ba shi haɗin kai ko da an ga kuma ya yi kuskure, akwai abin da za a je a gaya masa, a gaya masa ta private , in wanda ya kama mu iyaye za mu gaya masa ne, za mu gaya masa ta private , kar a tozarta masa rayuwa. In aka tozarta Ali, an tozarta industiri ɗin. “Ina yi mana fatan alkhairi. Mu na kuma jiran organisers su zo mana da wani sabon tsari da za a ci gaba. “Allah ya shi albarka, Allah ya yi mana albarka a kan abubuwan da mu ka sa a gaba baki ɗaya.”

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)